isah ayagi kasuwar bukata şarkı sözleri
Isah ayagi ne
Hoo ooo ahh ha ha
Komai nake yi ba ke ba
Me yasa ne kike haka
Menene baki samu ba
A kulawa ta duka
Soyayya ce na baki
Tun daga ruhi da zuciya
Kin san sai da yardar ki
Kafin mu fara soyayya
Bayyana miki matsayi na
Ki ka yarda ba wani jayayya
Toh yanzu kin sake
Kin sake
Toh nima na sake
So kasuwar bukata ce
Wanda ya soka ka so shi
Wanda ya kika indai ka bishi
Toh zaya saka a matsala
Eh wanin hanin ga allah baiwa ne
Kyan hali jari
Mai sonka sanda kake wahala
Shi ya hau tsari
Wanda yake gudu naka dan tsanani
Bai da alkairi
Dukan wata dama na baki
Ke a ranki kwai buri
Na lura da take-taken ki
Kin fi kwalba sharri
Alhamdulillah ga wata na samo
Duk ku zo ku kalla
Madadin ta na nemo
Daidai da zuciyata ce
Akan in rasata zan zauce
Ni da ke da nissan tafiya
Ga alama na hango
Tafiyar mu ba wata gajiya
Gun ki zana zam bango
Komai nake bida gunki
Take zaki ce ungo
Ashe rai sai da soyayya
Soyayya
So igiyar tsakar hanya
Kada yara har manya
So mai shiga cikin zuriya
Yai fada da tarbiya
Ni yanzu damuwa na manta
Nayo gamo da babbar mata
Duka zuciyarta ta ban kyauta
Yau zana toshe kunne
Dukan zuga ne akan ki ban dauka
Kowa ya ja zaren aibata ki
Duk karfi nasa zan tsinka
Na daura damarar kare ki
Ko da ko zana sha duka
Komai yawa da girman laifin ki
Zance a barki in dauka
Da zuciya ko rigace
Da na ciro na hannu na
In baki dan kiyo sawa
Ke ma ki bani mai sona
A jikina in sanya
Ki zamto madubina

