isah ayagi tambaya şarkı sözleri
So ya sanyaa...
Isah Ayagi ne
Hayya hayya
Eh ni tambaya nake yiwa
Zuciya ki ban bayani
Ga ki kadan cikin jikina
Amma kina wahal ni
Na lura har kwakwalwa
Kece ki ke saka ta tunani
Kina yawan dorani a sama
Sannan ki janye tsani
Nakan yawan raka ki
Amma ki kaini ki baroni
Ashe mutum idan ya kamu da so
Abun tausayi ne
Fage na so dukka ilimi naka
In ka zo dalibi ne
Duk timbatsa ta shehi
In ya iso ta shi hadimi ne
Lallai so hadari ne
Wani sa'in garkuwa ne
Tun farkon dan adam ko
So shi ke ja mai wahala
In na bi tarihi ance
Kabila shi ya kashe habila
So ba addini bane ba
Ya kashe arna har masu sallah
Shi ba yare bane ba
Manazarta na tai mai makala
Hmm wayyo Ni allah
Har ya samin kasala
Shi ba doka bane ba
Gashi rubuce cikin Constitution
Dan an san hadarin sa
Ya fi abortion da prostitution
So domin matsayin sa
Gashi cikin tsarin institution
Malamai koyar da shi su ke
Har ma ka ga sun bada question
Shi ba certificate ba
Gashi anayi mai lamination
Lallai so ya zamo
Kamar rana mai rarraba aiki
Ya zama hantsi gida na kowa
Ya shiga daki da daki
Shi so sunan sa sarki
Har yau shi ke da mulki
Duk izzar ka in ka zo gunsa
Dole ne za ka girmama shi
Duk zafin ranka in ka zo gun sa
Yanzu sai a ga kayi taushi
Da arahar ka da ka iso gunsa
Ya daga ka kayo farashi
Sai ya baka dariya
Wani sa'ilin sai ya baka haushi
Mai nazarin so yana da fadi
Ga shi da 'yaya kama da ridi
Shin wanne za'a fasa
Mutuwace ko hisabi
In dai har zaka rayu
Toh so baya kyale kalbi
Kuma ba kayi ka fasa
Ko zai zo ma da aibi
Ba ka duban asara
Domin neman habibi
So mai aiki da zabi
Wani sa'in hatsabibi
So na roke ka in ka azani
Toh sauke ni sannu
Tausaya min kar hawaye
Ya zamo yayyafin idanu
So ya sanyaa...
Nake baya ni

