S Piano Kano

KO DA KUDI KO BABU ANNABI NE SAMAN DUK HALITTAR ALLAH

s piano kano ko da kudi ko babu annabi ne saman duk halittar allah şarkı sözleri

Ko da kudi ko ba kudi Indai da Annabi Shikenan Annabi ne saman duk halittar Allah Banji tamkar yashiba Almuhiyi iyamin na dora Ban damarka allah tabara Zanyi abinda kaine ka fara In ka aminta bazan gazaba Kara dubun salati mujibu Ga wanda gunka yazam habibu Wanda muke ta nuna wa hubbu Bumu san randa zamu bari ba Sa ahlai kasa har suhabu Sa shurafa jinin mahabubu Gaida uwa darai koko babu Zan tafi zanyi bazan tsaya ba Kece asalin zuciyar sa Tsokar shugaba tajikin sa Umma abunda raina ya kun sa In na bida bazaki hana ba Cikin ladab da kas dakai na fara Annabi ganinan ba dabara Sai tsantsa ta kaunarka nura Mai hasken da ba zai gushe ba Kafi gaban sanin duk halitta Balle ma baki ya furta Annabi kai kadai ka dayan ta Allah baiyi tamkar ya kai ba Komai daga shi muka samu In mun roki Allah ya bamu Sai munzo dakai ya imamu Sannan rabbana zaiyi duba Maiwa kaunu mai yiwa Allah Kai ka sanar damu rabbu Allah Badan kaiba wallahi Allah Da baa san akwai rabbana ba Jeka abinka rainon halima Muko mudinga yima walima Tilas kaunu tassalama ma Bayan kai baayiyo gwani Ko musa dakai aka bashi Isah sai dakai aka sanshi Kyan yusuf ko kaine ba bashi Allah baiyi ma kishiya ba Ban tabajin kamar shugaba ba Gun girma baayo yashiba Kai bari buncike karka duba Baza ka san kamar shugaba ba Nai nazari kadan take nace Ko tafiyar sa ma ta daban ce Cif cif yake ga kwatance Komai nasa ba namu neba Ga hasken hakora gareshi Da ya taho guri kaji kamshi Dole na raira baiti gareshi Nayi ta fada baayiyo yashiba Suyi masa sharri yayi musu khairi Mai kyautar da sam baya gori Kai kusa sani ashe rai da buri Buri na yayimin maraba Ce na taho ziyara madina Inzo gunka ya dan amina Dan fadima cene na zauna Na roka bazaka gaza ba Zana takaita baitin na huta Koda da tambayar wanda yayi ta Sunusi piano zoo road yayi ta Ni da hubbu ba wani ne ba To aikin ka ne zuljalu Kara dubu dubu gun salahu Wanda ya zarce kowa a sulhu Abban fadima mahabuba Karshe addu a ta ka amsa Duk makiyan mu sasu su kasa Duk mai sharri komar shi kansa Barmu da sayyada umma abba
Sanatçı: S Piano Kano
Türü: Belirtilmemiş
Ajans/Yapımcı: Belirtilmemiş
Şarkı Süresi: 4:43
Toplam: kayıtlı şarkı sözü
S Piano Kano hakkında bilgi girilmemiş.

Fotoğrafı